Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : ya bada rahoton cewa an gudanar da taron tunawa da kuma girmama wadanna shahidai ne a wurin da suka yi shahada a kudancin Tehran, a ranar 30 ga watan Augustan shekara 1981 shekaru 40 da suka gabata.
Tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan Iran a shekara 1979 ‘yan ta’adda su fara kashe jami’an gwamnatin kasar, kuma kungiyoyin ‘yan ta’adda wadanda suka hada da kungiyar MKO ko Mujahidun Khalkh ne suka gaba a wannan ta’asar. MKO dai a halin yanzu ta na samun kariya daga kasashen yamma karkashin tutar wadanda aka zalunta.
Kungiyar ta sha kai hare-hare kan fararen hula da jami’an gwamnatin JMI, daga ciki har da dana bom da tada shi a ofishin firai ministan kasar Iran na Lokacin wanda ya kai shahadar mutane da dama daga ciki har da shi shugaban kasa Ali Rajai da firai ministansa Bahonar.
Mai maga a taron tuna wadannan shahidai a yau Litinin, mataimakin shugaban kasa a kan al-amuran majalisar dokoki Mohammad Hussain ya bayyana cewa kungiyar munafukai ta MKO ta kashe mutane kimani 17,000 a kasar Iran.
342/